Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:36

[1] Kalmomin Malami, ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima.

[2] “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami. “Gaba ɗaya ba amfani! Kome ba shi da amfani!”

[3] Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar da yake fama a duniya?

[4] Zamanai sukan zo zamanai su wuce, amma duniya tana nan har abada.

[5] Rana takan fito rana ta kuma fāɗi, ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.

[6] Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.

[7] Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika. Daga inda rafuffukan suke fitowa, a can suke komawa kuma.

[8] Dukan abubuwa suna kawo gajiya, gaban magana. Ido ba ya gaji da gani, haka ma kunne yă ƙoshi da ji.

[9] Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance, abin da aka yi za a sāke yi kuma; babu wani abu sabo a duniya.

[10] Akwai wani abin da za a ce, “Duba! Ga wani abu sabo”? Abin yana nan, tun dā can, ya kasance kafin lokacinmu.

[11] Ba a tunawa da mutanen dā, haka su ma da ba a haifa ba tukuna waɗanda za su biyo bayansu ba za a tuna da su ba.

[12] Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima.

[13] Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane!

[14] Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.

[15] Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba; ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.

[16] Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.”

[17] Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.

[18] Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki; yawan sani, yawan ɓacin rai.

Mai Hadishi — Chapters