Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:17

[1] Maganganun Agur ɗan Yake, magana ce horarriya. Wannan mutum ya furta wa Itiyel da kuma ga Ukal,

[2] “Ni ne mafi jahilci a cikin mutane; ba ni da fahimi irin na mutum.

[3] Ban koyi hikima ba, ba ni kuma da sani game da Mai Tsarkin nan,

[4] Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani!

[5] “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.

[6] Kada ka ƙara ga maganarsa, in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne.

[7] “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji; kada ka hana ni kafin in mutu.

[8] Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.

[9] In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.

[10] “Kada ka baza ƙarairayi game da bawa ga maigidansa, in ba haka ba, zai la’ance ka, za ka kuwa sha wahala a kan haka.

[11] “Akwai waɗanda sukan zagi mahaifinsu ba sa kuma sa wa mahaifiyarsu albarka;

[12] waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su;

[13] waɗanda kullum idanunsu masu kallon reni ne, waɗanda kallon da suke yi na daurin gira ne;

[14] waɗanda haƙoransu takuba ne waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne don su cinye matalauta daga duniya da kuma mabukata daga cikin mutane.

[15] “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’

[16] Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’

[17] “Idon da yake yi wa mahaifi ba’a, wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya, hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido, ungulai za su cinye su.

[18] “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,

[19] yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.

[20] “Ga yadda mazinaciya take yi. Takan ci ta share bakinta ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’

[21] “Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki, abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa,

[22] bawan da ya zama sarki, wawan da ya ƙoshi da abinci,

[23] macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji, da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta.

[24] “Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana, duk da haka suna da hikima ƙwarai.

[25] Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;

[26] remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;

[27] fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;

[28] ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.

[29] “Akwai abubuwa uku da suke jan jiki da kuma taƙama a tafiyarsu abubuwa huɗu waɗanda suke kwarjini da taƙama a tafiyarsu,

[30] zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa;

[31] zakara mai taƙama, da bunsuru, da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi.

[32] “In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka, ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta, ka dāfa hannunka a bisa bakinka!

[33] Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.”

Karin Magana — Chapters