Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:32

[1] Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara.

[2] Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne.

[3] Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika.

[4] Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa;

[5] ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci.

[6] Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki, kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane;

[7] gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka

[8] kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya?

[9] In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani,

[10] in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba.

[11] Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa.

[12] Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.

[13] Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi.

[14] Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa.

[15] Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi.

[16] In ka sami zuma, ka sha isashe kawai, in ya yi yawa, za ka yi amai.

[17] Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka.

[18] Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.

[19] Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala.

[20] Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki.

[21] In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha.

[22] Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka.

[23] Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.

[24] Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.

[25] Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa.

[26] Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye.

[27] Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa, haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka.

[28] Kamar birni da katangarsa sun rushe haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa.

Karin Magana — Chapters