Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:10

[1] Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.

[2] Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.

[3] Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.

[4] Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.

[5] Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu.

[6] Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.

[7] Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka; dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome.

[8] Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala, sai ta dawo wa mugu a maimako.

[9] Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta.

[10] Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki; sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki.

[11] Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin.

[12] Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci, amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.

[13] Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.

[14] Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.

[15] Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala, amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa.

[16] Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya.

[17] Mutumin kirki kan ribance kansa, amma mugu kan kawo wa kansa wahala.

[18] Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.

[19] Mutum mai adalci da gaske yakan sami rai, amma shi da ya duƙufa ga aikata mugunta kan tarar da mutuwarsa.

[20] Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.

[21] Ka tabbata da wannan. Mugaye ba za su tafi babu hukunci ba, amma waɗanda suke masu adalci za su tafi babu hukunci.

[22] Kamar zinariya a hancin alade haka kyan mace wadda ba ta da hankali.

[23] Sha’awar adalai kan ƙare kawai a aikata alheri, amma sa zuciyar mugaye kan ƙarasa kawai a fushi.

[24] Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.

[25] Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.

[26] Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada, amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar.

[27] Duk mai nema alheri kan sami alheri, amma mugu kan zo wa wanda yake nemansa.

[28] Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi, amma adali zai yi nasara kamar koren ganye.

[29] Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai, kuma wawa zai zama bawan masu hikima.

[30] ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.

[31] In masu adalci sun sami abin da ya dace da su a duniya, yaya zai zama ga marasa sanin Allah da kuma masu zunubi!

Karin Magana — Chapters