Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:53

[1] Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka,

[2] ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne.

[3] Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne.

[4] Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.

[5] Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.

[6] Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;

[7] gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.

[8] Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.

[9] Kada ka yi magana da wawa, gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a.

[10] Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu,

[11] gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu.

[12] Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.

[13] Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.

[14] Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.

[15] Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna;

[16] cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.

[17] Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.

[18] Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.

[19] Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.

[20] Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,

[21] gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

[22] Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.

[23] Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi.

[24] Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

[25] Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!

[26] Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,

[27] gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.

[28] Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.

[29] Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?

[30] Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.

[31] Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!

[32] A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.

[33] Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.

[34] Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa.

[35] Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”

Karin Magana — Chapters