Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:33

[1] An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.

[2] Mawadaci da matalauci suna da abu guda. Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.

[3] Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka, amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala.

[4] Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.

[5] A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.

[6] Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

[7] Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.

[8] Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa.

[9] Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.

[10] Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.

[11] Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne zai zama aminin sarki.

[12] Idanun Ubangiji na lura da sani, amma yakan ƙi kalmomin marar aminci.

[13] Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”

[14] Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi; duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.

[15] Wauta tana da yawa a zuciyar yara, amma sandar horo zai kore ta nesa da su.

[16] Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

[17] Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima; ka yi amfani da abin da nake koyarwa,

[18] gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.

[19] Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji, ina koya maka yau, har kai ma.

[20] Ban rubuta maka maganganu talatin ba, maganganun shawara da sani,

[21] ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai, saboda ka iya ba da amsa daidai ga duk wanda ya aike ka?

[22] Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,

[23] gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su.

[24] Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,

[25] in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.

[26] Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi;

[27] gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.

[28] Kada ka matsar da shaidar kan iyakar da kakanninka suka kafa.

[29] Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.

Karin Magana — Chapters