[1] Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai.
[2] Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta.
[3] Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin.
[4] “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali.
[5] “Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye.
[6] Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.
[7] “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.
[8] Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.
[9] Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima; ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.
[10] “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
[11] Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa, za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
[12] In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada; in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.”
[13] Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.
[14] Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,
[15] tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.
[16] “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.
[17] “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”
[18] Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.