Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:11

[1] Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,

[2] in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,

[3] to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka!

[4] Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma.

[5] Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.

[6] Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

[7] Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki,

[8] duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

[9] Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku?

[10] Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,

[11] talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.

[12] Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,

[13] wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,

[14] wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye

[15] Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.

[16] Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

[17] duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

[18] zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

[19] mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

[20] Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

[21] Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka.

[22] Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.

[23] Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce,

[24] suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci.

[25] Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.

[26] Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta, mazinaciya kuma takan farauci ranka.

[27] Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa ba tare da rigunansa sun ƙone ba?

[28] Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?

[29] Haka yake da wanda ya kwana da matar wani; babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.

[30] Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.

[31] Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.

[32] Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali; duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.

[33] Dūka da kunya ne za su zama rabonsa, kuma kunyarsa za tă dawwama.

[34] Gama kishi kan tā da hasalar miji, kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.

[35] Ba zai karɓi duk wata biya ba; zai ƙi cin hanci, kome yawansu.

Karin Magana — Chapters