Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:08

[1] Hikima ba ta yin kira ne? Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?

[2] A ƙwanƙoli a kan hanya, inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;

[3] kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya,

[4] “Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan ’yan adam.

[5] Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali; ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.

[6] Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa; na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai.

[7] Bakina yana magana abin da yake gaskiya, gama leɓunana sun ƙi mugunta.

[8] Dukan kalmomin bakina suna da adalci; babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne.

[9] Ga mai tunani dukansu daidai ne; ba su da laifi ga waɗanda suke da sani.

[10] Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa, sani a maimakon zinariya zalla,

[11] gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.

[12] “Ni, hikima, ina zama tare da hankali; ina da sani da iya rarrabewa.

[13] Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.

[14] Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko.

[15] Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;

[16] ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.

[17] Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.

[18] Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama.

[19] ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.

[20] Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya,

[21] ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika.

[22] “Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni;

[23] an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance.

[24] Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa;

[25] kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni,

[26] kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya.

[27] Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,

[28] sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,

[29] sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.

[30] A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa,

[31] ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam.

[32] “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.

[33] Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima; kada ku ƙyale ta.

[34] Mai albarka ne wanda ya saurare ni; yana tsaro kullum a ƙofofina, yana jira a ƙofar shigata.

[35] Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

[36] Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa; dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”

Karin Magana — Chapters