Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:05

[1] Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.

[2] Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa.

[3] Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.

[4] Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.

[5] Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.

[6] Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.

[7] Leɓunan basira ba su dace da wawa ba, ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!

[8] Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara.

[9] Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.

[10] Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.

[11] Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu.

[12] Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.

[13] In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.

[14] Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.

[15] Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.

[16] Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa, da yake ba shi da sha’awar samun hikima?

[17] Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.

[18] Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.

[19] Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.

[20] Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba; duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.

[21] Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki babu farin ciki ga mahaifin wawa.

[22] Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.

[23] Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce don yă lalace yin adalci.

[24] Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima, amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.

[25] Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.

[26] Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu.

[27] Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne.

[28] Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.

Karin Magana — Chapters