Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:59

[1] Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.

[2] Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.

[3] Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu.

[4] Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.

[5] Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.

[6] Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu.

[7] Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe.

[8] Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci.

[9] Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.

[10] Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci.

[11] Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.

[12] Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.

[13] Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne.

[14] Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.

[15] Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci.

[16] Hakkin adalai kan kawo musu rai, amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci.

[17] Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.

[18] Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.

[19] Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.

[20] Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani.

[21] Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.

[22] Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai.

[23] Wawa yakan ji daɗi halin mugunta, amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima.

[24] Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi; abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata.

[25] Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye, amma adalai za su tsaya daram har abada.

[26] Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.

[27] Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye.

[28] Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki, amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.

[29] Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.

[30] Ba za a taɓa tumɓuke masu adalci ba, amma mugaye ba za su ci gaba da kasance a ƙasar ba.

[31] Bakin adalai kan fitar da hikima, amma za a dakatar da mugun harshe.

[32] Leɓunan adalai sun san abin da ya dace, amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai.

Karin Magana — Chapters