[1] Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
[2] gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata.
[3] Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.
[4] Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
[5] Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
[6] cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
[7] Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
[8] Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka.
[9] Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
[10] ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
[11] Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,
[12] domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
[13] Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi,
[14] gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya.
[15] Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
[16] Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
[17] Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne.
[18] Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
[19] Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
[20] ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa.
[21] Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira, kada ka bar su su rabu da kai;
[22] za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka.
[23] Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya, ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
[24] sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
[25] Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
[26] gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
[27] Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka.
[28] Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.
[29] Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai.
[30] Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba.
[31] Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.
[32] Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.
[33] La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali.
[34] Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri.
[35] Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.