[1] Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne.
[2] Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo.
[3] Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta, amma ba za a tumɓuke adali ba.
[4] Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.
[5] Shirye-shiryen masu adalci daidai ne, amma shawarar mugaye ruɗu ne.
[6] Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai, amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su.
[7] Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu, amma gidan masu adalci kan tsaya daram.
[8] Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa, amma mutane marasa azanci akan rena su.
[9] Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci.
[10] Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
[11] Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
[12] Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka.
[13] Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi, amma adali kan kuɓuta daga wahala.
[14] Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada.
[15] Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara.
[16] Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi.
[17] Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya, amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
[18] Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
[19] Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
[20] Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
[21] Ba wani lahanin da zai sami masu adalci, amma mugaye suna da nasu cike da wahala.
[22] Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
[23] Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa, amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci.
[24] Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
[25] Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai.
[26] Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
[27] Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.
[28] A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa.