Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:49

[1] Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.

[2] Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.

[3] Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa, amma leɓunan masu hikima kan tsare su.

[4] Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.

[5] Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.

[6] Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome, amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.

[7] Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.

[8] Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu, amma wautar wawaye ruɗu ne.

[9] Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi, amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya.

[10] Kowace zuciya ta san ɓacin ranta, kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa.

[11] Za a rushe gidan mugu, amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka.

[12] Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.

[13] Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo, kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki.

[14] Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu, kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa.

[15] Marar azanci kan gaskata kome, amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa.

[16] Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta, amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje.

[17] Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta, akan kuma ƙi mai son nuna wayo.

[18] Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani.

[19] Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai.

[20] Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa.

[21] Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.

[22] Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.

[23] Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.

[24] Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.

[25] Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.

[26] Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.

[27] Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.

[28] Yawan mutane shi ne ɗaukakar sarki, amma in ba tare da mabiya ba sarki ba kome ba ne.

[29] Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.

[30] Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo.

[31] Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.

[32] Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi, amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka.

[33] Hikima tana a zuciyar mai azanci, kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa.

[34] Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.

[35] Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima, amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa.

Karin Magana — Chapters