[1] A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so.
[2] Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya.
[3] Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
[4] Girmankai da fariya, su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne!
[5] Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
[6] Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
[7] Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai.
[8] Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya.
[9] Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
[10] Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta; maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi.
[11] Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani.
[12] Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu.
[13] In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.
[14] Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
[15] Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci amma fargaba ga masu aikata mugunta.
[16] Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu.
[17] Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.
[18] Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya.
[19] Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.
[20] A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.
[21] Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.
[22] Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.
[23] Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.
[24] Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun.
[25] Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
[26] Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.
[27] Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!
[28] Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka, kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.
[29] Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.
[30] Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji.
[31] Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.