Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:52

[1] Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.

[2] Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani, ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya.

[3] Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi.

[4] Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi.

[5] Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.

[6] Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.

[7] ’Yan’uwan matalauci sukan guje shi, balle abokansa, su ma za su guje shi. Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo, ba zai sam su ba.

[8] Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.

[9] Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.

[10] Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba, haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki!

[11] Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.

[12] Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.

[13] Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.

[14] Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne.

[15] Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.

[16] Duk wanda ya bi umarnai kan tsare ransa, amma duk wanda ya ƙi binsu zai mutu.

[17] Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.

[18] Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya; kada ka goyi baya lalacewarsa.

[19] Dole mai zafin rai yă biya tara; in ka fisshe shi sau ɗaya, to, sai ka sāke yin haka.

[20] Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.

[21] Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika.

[22] Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa; gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.

[23] Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.

[24] Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!

[25] Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari; ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani.

[26] Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.

[27] In ka daina jin umarni, ɗana, za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.

[28] Mai shaidar da yake malalaci yana wa shari’a ba’a ne, bakin mugaye kuma na haɗiye mugunta.

[29] An shirya tara saboda masu ba’a ne, dūka kuma saboda bayan wawaye.

Karin Magana — Chapters