[1] Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
[2] kana kasa kunne ga abin da yake na hikima, kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
[3] in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
[4] in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
[5] to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah.
[6] Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
[7] Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
[8] gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
[9] Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.
[10] Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai.
[11] Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora.
[12] Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,
[13] waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,
[14] waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,
[15] waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.
[16] Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,
[17] wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.
[18] Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.
[19] Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.
[20] Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.
[21] Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;
[22] amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta.