Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:18

[1] Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata ka saurara da kyau ga kalmomin basirata,

[2] don ka ci gaba da yin kome daidai leɓunanka za su adana sani.

[3] Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai;

[4] amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.

[5] Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.

[6] Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.

[7] Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa.

[8] Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta,

[9] don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani,

[10] don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.

[11] A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.

[12] Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!

[13] Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni.

[14] Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.”

[15] Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku.

[16] In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?

[17] Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi.

[18] Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

[19] Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

[20] Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani?

[21] Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.

[22] Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.

[23] Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce.

Karin Magana — Chapters