[1] Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa, amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.
[2] Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau, amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye.
[3] Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa, amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.
[4] Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
[5] Adali yana ƙin abin da yake ƙarya, amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.
[6] Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
[7] Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai.
[8] Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana.
[9] Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai, amma fitilar mugaye mutuwa take.
[10] Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
[11] Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
[12] Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo, amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
[13] Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
[14] Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
[15] Fahimta mai kyau kan sami tagomashi, amma hanyar marar aminci tana da wuya.
[16] Kowane mai azanci yakan nuna sani, amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.
[17] Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.
[18] Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.
[19] Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai, amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.
[20] Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
[21] Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali.
[22] Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa, amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.
[23] Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace, amma rashin adalci kan share shi tas.
[24] Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
[25] Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa.