Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:26

[1] Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba.

[2] Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.

[3] Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye!

[4] Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.

[5] Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.

[6] Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.

[7] Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas haka karin magana yake a bakin wawa.

[8] Kamar ɗaura dutse a majajjawa haka yake da girmama wawa.

[9] Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa.

[10] Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.

[11] Kamar yadda kare kan koma ga amansa, haka wawa kan maimaita wautarsa.

[12] Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.

[13] Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”

[14] Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa.

[15] Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.

[16] Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.

[17] Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.

[18] Kamar yadda mahaukaci yake harbin cukwimai ko kibiyoyi masu dafi

[19] haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”

[20] In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.

[21] Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.

[22] Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum.

[23] Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba haka leɓuna masu mugun zuciya.

[24] Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa, amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci

[25] Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi, gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.

[26] Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya, duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.

[27] In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki; in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.

[28] Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.

Karin Magana — Chapters