Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:38

[1] Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi.

[2] Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.

[3] Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,

[4] ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.

[5] Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.

[6] Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.

[7] Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.

[8] Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.

[9] Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”

[10] Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.

[11] Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi.

[12] Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba.

[13] Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne.

[14] Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.

[15] Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.

[16] Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani.

[17] Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su.

[18] Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.

[19] Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe.

[20] Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina.

[21] Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka;

[22] gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum.

[23] Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka, gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.

[24] Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.

[25] Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.

[26] Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai.

[27] Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.

Karin Magana — Chapters