[1] Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne; duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
[2] Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.
[3] Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.
[4] Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
[5] Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne, amma mutum mai basira yakan jawo su.
[6] Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
[7] Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi; masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
[8] Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a, yakan ga dukan mugunta da idanunsa.
[9] Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki; ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”?
[10] Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.
[11] Akan san ƙananan yara ta ayyukansu, ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.
[12] Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani, Ubangiji ne ya yi su duka.
[13] Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
[14] “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.
[15] Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.
[16] A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
[17] Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
[18] Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa.
[19] Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
[20] In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.
[21] Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.
[22] Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.
[23] Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.
[24] Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?
[25] Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
[26] Sarki mai hikima yakan gane mugunta; ya hukunta su ba tausayi.
[27] Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum takan bincika lamirinsa.
[28] Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya; ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.
[29] Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi.
[30] Naushi da rauni kan share mugunta, dūka kuma kan tsabtacce lamiri.