[1] Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.
[2] Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.
[3] Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka.
[4] Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka;
[5] za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.
[6] A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka.
[7] Sai na gani a cikin marasa azanci, na lura a cikin samari, wani matashi wanda ba shi da hankali.
[8] Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta, yana tafiya a gefen wajen gidanta
[9] da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa, yayinda duhun dare yana farawa.
[10] Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi, saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.
[11] (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida;
[12] wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.)
[13] Sai ta kama shi ta rungume shi da duban soyayya a fuskarta ta ce,
[14] “Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina.
[15] Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka!
[16] Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
[17] Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa.
[18] Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!
[19] Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.
[20] Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”
[21] Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
[22] Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
[23] sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.
[24] Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
[25] Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
[26] Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
[27] Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.