Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:05

[1] Benyamin shi ne mahaifin, Bela ɗansa na fari, Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku,

[2] Noha na huɗu da Rafa na biyar.

[3] ’Ya’yan Bela maza su ne, Addar, Gera, Abihud

[4] Abishuwa, Na’aman, Ahowa,

[5] Gera, Shefufan da Huram.

[6] Waɗannan su ne zuriyar Ehud, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Geba waɗanda aka kuma kwasa zuwa Manahat.

[7] Na’aman, da Ahiya, da Gera. Gera ne shugabansu lokacin da aka kai su bauta, shi ne ya haifi Uzza da Ahilud.

[8] An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara.

[9] Ya haifi Yobab, Zibiya, Hodesh, Malkam,

[10] Yewuz, Sakiya da Mirma ta wurin Hodesh matarsa. Waɗannan su ne ’ya’yansa, kawunan iyalai.

[11] Ya haifi Abitub da Efa’al ta wurin Hushim.

[12] ’Ya’yan Efa’al maza su ne, Eber, Misham, Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan kewayensu),

[13] da Beriya da Shema, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Aiyalon waɗanda kuma suka kori mazaunan Gat.

[14] Ahiyo, Shashak, Yeremot

[15] Zebadiya, Arad, Eder,

[16] Mika’ilu, Isfa da Yoha su ne ’ya’yan Beriya maza.

[17] Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber,

[18] Ishmerai, Izliya da Yobab su ne ’ya’yan Efa’al maza.

[19] Yakim, Zikri, Zabdi,

[20] Eliyenai, Zilletai, Eliyel,

[21] Adahiya, Berahiya da Shimra su ne ’ya’yan Shimeyi maza.

[22] Ishfan, Eber, Eliyel,

[23] Abdon, Zikri, Hanan,

[24] Hananiya, Elam, Antotiya,

[25] Ifdehiya da Fenuwel su ne ’ya’yan Shashak maza.

[26] Shamsherai, Shehariya, Ataliya,

[27] Ya’areshiya, Iliya da Zikri su ne ’ya’yan Yeroham maza.

[28] Dukan waɗannan su ne kawunan iyalai, manya kamar yadda aka lissafta a cikin zuriyarsu, suka zauna a Urushalima.

[29] Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Sunan matarsa Ma’aka,

[30] ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,

[31] Gedor, Ahiyo, Zeker

[32] da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.

[33] Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.

[34] Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda ya zama mahaifin Mika.

[35] ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tereya da Ahaz.

[36] Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.

[37] Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel.

[38] Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan ’ya’yan Azel maza ne.

[39] ’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne, Ulam ɗan farinsa, Yewush ɗansa na biyu da Elifelet na uku.

[40] ’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da ’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya. Dukan waɗannan zuriyar Benyamin ne.

1 Tarihi — Chapters