Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 7:08

[1] Adamu, Set, Enosh,

[2] Kenan, Mahalalel, Yared,

[3] Enok, Metusela, Lamek, Nuhu.

[4] ’Ya’yan Nuhu maza su ne, Shem, Ham da Yafet.

[5] ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.

[6] ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat da Togarma.

[7] ’Ya’yan Yaban maza su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.

[8] ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana.

[9] ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza su ne, Sheba da Dedan

[10] Kush shi ne mahaifin Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.

[11] Masar shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa,

[12] Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa.

[13] Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa,

[14] Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa

[15] Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,

[16] Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa.

[17] ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Meshek.

[18] Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuwa shi ne mahaifin Eber.

[19] Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan.

[20] Yoktan shi ne mahaifin Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera

[21] Hadoram, Uzal, Dikla,

[22] Ebal, Abimayel, Sheba,

[23] Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.

[24] Shem, Arfakshad, Shela,

[25] Eber, Feleg, Reyu

[26] Serug, Nahor, Tera

[27] da Abram (wato, Ibrahim).

[28] ’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel.

[29] Waɗannan su ne zuriyarsu. Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam,

[30] Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema

[31] Yetur, Nafish da Kedema. Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza.

[32] ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan.

[33] ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.

[34] Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila.

[35] ’Ya’yan Isuwa maza, su ne, Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora

[36] ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz, da Timna wanda aka haifa wa Amalek.

[37] ’Ya’yan maza Reyuwel su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza.

[38] ’Ya’yan Seyir maza su ne, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.

[39] ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan.

[40] ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana.

[41] Ɗan Ana shi ne, Dishon. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.

[42] ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.

[43] Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.

[44] Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.

[45] Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.

[46] Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.

[47] Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.

[48] Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.

[49] Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.

[50] Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab.

[51] Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet

[52] Oholibama, Ela, Finon

[53] Kenaz, Teman, Mibzar,

[54] Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.

1 Tarihi — Chapters