[1] ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
[2] ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
[3] Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
[4] Eleyazar shi ne mahaifin Finehas, Finehas mahaifin Abishuwa,
[5] Abishuwa mahaifin Bukki, Bukki mahaifin Uzzi,
[6] Uzzi mahaifin Zerahiya, Zerahiya mahaifin Merahiyot,
[7] Merahiyot mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,
[8] Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Ahimawaz,
[9] Ahimawaz mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Yohanan,
[10] Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima),
[11] Azariya mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,
[12] Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum,
[13] Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya,
[14] Azariya mahaifin Serahiya, Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak.
[15] Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.
[16] ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari.
[17] Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Gershom. Libni da Shimeyi.
[18] ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
[19] ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu.
[20] Na Gershom su ne, Libni, Yahat, Zimma,
[21] Yowa, Iddo, Zera da Yeyaterai.
[22] Zuriyar Kohat su ne, Amminadab, Kora, Assir,
[23] Elkana, Ebiyasaf, Assir,
[24] Tahat, Uriyel, Uzziya da Shawulu.
[25] Zuriyar Elkana su ne, Amasai, Ahimot,
[26] Elkana, Zofai, Nahat,
[27] Eliyab Yeroham, Elkana da Sama’ila.
[28] ’Ya’yan Sama’ila maza su ne, Yowel ɗan fari da Abiya ɗa na biyu.
[29] Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza,
[30] Shimeya, Haggiya da Asahiya.
[31] Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
[32] Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
[33] Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,
[34] ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa,
[35] ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,
[36] ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya
[37] ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,
[38] ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;
[39] da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,
[40] ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya, ɗan Malkiya,
[41] ɗan Etni, ɗan Zera, ɗan Adahiya
[42] ɗan Etan, ɗan Zimma, ɗan Shimeyi,
[43] ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi;
[44] da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk,
[45] ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,
[46] ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,
[47] ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.
[48] Aka ba ’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah.
[49] Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.
[50] Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa,
[51] Bukki, Uzzi, Zerahiya,
[52] Merahiyot, Amariya, Ahitub,
[53] Zadok da Ahimawaz.
[54] Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):
[55] Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.
[56] Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne.
[57] Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,
[58] Hilen, Debir,
[59] Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.
[60] Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.
[61] Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.
[62] Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.
[63] Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
[64] Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.
[65] Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.
[66] Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.
[67] A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer,
[68] Yokmeyam, Bet-Horon,
[69] Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.
[70] Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.
[71] Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;
[72] daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat,
[73] Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;
[74] daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon,
[75] Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;
[76] daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.
[77] Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;
[78] daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,
[79] Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;
[80] daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim,
[81] Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.