Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:55

[1] Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.

[2] Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.

[3] Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.

[4] Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.

[5] Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.

[6] Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.

[7] Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya,

[8] na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim,

[9] na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin,

[10] na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya,

[11] na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya,

[12] na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim,

[13] na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,

[14] na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer,

[15] na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez,

[16] na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel,

[17] na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul,

[18] na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.

[19] Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.

[20] Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.

[21] Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.

[22] Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.

[23] ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.

[24] Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga ’ya’yan Mika maza, Shamir.

[25] Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.

[26] ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.

[27] ’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.

[28] Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.

[29] Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel.

[30] Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.

[31] Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.

1 Tarihi — Chapters