[1] Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000.
[2] Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[3] Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko.
[4] Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[5] Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa.
[6] Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa.
[7] Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[8] Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[9] Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[10] Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[11] Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[12] Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[13] Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[14] Na goma sha ɗaya, don wata goma sha ɗaya, shi ne Benahiya mutumin Firaton, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[15] Na goma sha biyu don wata goma sha biyu, shi ne Heldai mutumin Netofa, daga iyalin Otniyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
[16] Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila, bisa mutanen Ruben su ne, Eliyezer ɗan Zikri; bisa mutanen Simeyon shi ne, Shefatiya ɗan Ma’aka
[17] bisa mutanen Lawi shi ne, Hashabiya ɗan Kemuwel; bisa mutanen Haruna shi ne, Zadok;
[18] bisa mutanen Yahuda shi ne, Elihu, ɗan’uwan Dawuda; bisa mutanen Issakar shi ne, Omri ɗan Mika’ilu;
[19] bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya; bisa mutanen Naftali shi ne, Yerimot ɗan Azriyel;
[20] bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya; bisa rabin kabilar Manasse shi ne, Yowel ɗan Fedahiya;
[21] bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya; bisa mutanen Benyamin shi ne, Ya’asiyel ɗan Abner;
[22] bisa mutanen Dan shi ne, Azarel ɗan Yeroham. Waɗannan su ne shugabanni a bisa kabilan Isra’ila.
[23] Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.
[24] Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba.
[25] Azmawet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ɗakuna ajiyar fada. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai lura da ɗakunan ajiya a yankuna, cikin garuruwa, ƙauyuka da kuma hasumiyoyin tsaro.
[26] Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da ma’aikatan gona waɗanda suke nome ƙasar.
[27] Shimeyi mutumin Ramat shi ne mai lura da gonakin inabi. Zabdi mutumin Shifam shi ne mai lura da amfanin gonakin inabi don matsin ruwan inabi.
[28] Ba’al-Hanan mutumin Geder shi ne mai lura da itatuwan zaitun da na al’ul a gindin tuddan yamma. Yowash shi ne mai lura da tanadin man zaitun.
[29] Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon. Shafat ɗan Adlai shi ne mai lura da garkuna a kwari.
[30] Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma. Yedehiya mutumin Meronot shi ne mai lura da jakuna.
[31] Yaziz mutumin Hagiri shi ne mai lura da tumaki. Dukan waɗannan shugabanni ne masu lura da mallakar Sarki Dawuda.
[32] Yonatan, kawun Dawuda, shi ne mashawarci, mutum mai hangen nesa kuma marubuci. Yehiyel ɗan Hakmoni ne ya lura da ’ya’yan sarki maza.
[33] Ahitofel shi ne mashawarcin sarki. Hushai mutumin Arkitawa shi ne abokin sarki na kud da kud.
[34] Yehohiyada ɗan Benahiya da Abiyatar ne suka gāji Ahitofel. Yowab shi ne shugaban mayaƙan masarauta.