Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:01

[1] Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila.

[2] Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa.

[3] Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas.

[4] Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.

[5] Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”

[6] Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.

[7] Na Gershonawa, Ladan da Shimeyi.

[8] ’Ya’yan Ladan maza su ne, Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.

[9] ’Ya’yan Shimeyi maza su ne, Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka. Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.

[10] ’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne, Yahat, Zina, Yewush da Beriya. Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.

[11] Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.

[12] ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.

[13] ’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.

[14] An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.

[15] ’Ya’yan Musa maza su ne, Gershom da Eliyezer.

[16] Zuriyar Gershom su ne, Shebuwel ne ɗan fari.

[17] Zuriyar Eliyezer su ne, Rehabiya ne ɗan fari. Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.

[18] ’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari.

[19] ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.

[20] ’Ya’yan Uzziyel maza su ne, Mika na fari da Isshiya na biyu.

[21] ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. ’Ya’yan Mali maza su ne, Eleyazar da Kish.

[22] Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su.

[23] ’Ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.

[24] Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.

[25] Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada,

[26] Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.”

[27] Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga ’yan shekara ashirin ko fiye.

[28] Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah.

[29] Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.

[30] Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma

[31] da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.

[32] A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.

1 Tarihi — Chapters