[1] Waɗannan su ne ’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun,
[2] Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher.
[3] ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.
[4] Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi ’ya’ya maza biyar ne.
[5] ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
[6] ’Ya’yan Zera maza su ne, Zimri, Etan, Heman, Kalkol da Darda, su biyar ne.
[7] ’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta.
[8] Ɗan Etan shi ne, Azariya.
[9] ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb.
[10] Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda.
[11] Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz,
[12] Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse.
[13] Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya,
[14] na huɗun Netanel, na biyar Raddai,
[15] na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda.
[16] ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel. ’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel.
[17] Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel.
[18] Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon.
[19] Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur.
[20] Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.
[21] Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.
[22] Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.
[23] (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.
[24] Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa.
[25] ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya.
[26] Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam.
[27] ’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker.
[28] ’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada. ’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur.
[29] Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid.
[30] ’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara.
[31] Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai.
[32] ’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara.
[33] ’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.
[34] Sheshan ba shi da ’ya’ya maza, sai ’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha.
[35] Sheshan ya ba da ’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai.
[36] Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad,
[37] Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed,
[38] Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya,
[39] Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa,
[40] Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum
[41] Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama.
[42] ’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron.
[43] ’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema.
[44] Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai.
[45] Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur.
[46] Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.
[47] ’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af.
[48] Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana.
[49] Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya. ’Yar Kaleb ita ce Aksa.
[50] Waɗannan su ne zuriyar Kaleb. ’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim,
[51] Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader.
[52] Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa,
[53] kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.
[54] Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa,
[55] kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab.