[1] Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;
[2] na ukun, Absalom ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;
[3] na biyar, Shefatiya ɗan Abital; da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla.
[4] Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida. Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,
[5] kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can. Shimeya, Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa ’yar Ammiyel ta haifa.
[6] Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet,
[7] Noga, Nefeg, Yafiya,
[8] Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka.
[9] Dukan waɗannan ’ya’yan Dawuda ne maza, ban da ’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce ’yar’uwarsu.
[10] Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat,
[11] da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,
[12] da Amaziya, da Azariya, da Yotam,
[13] da Ahaz, da Hezekiya da Manasse,
[14] da Amon, da Yosiya.
[15] ’Ya’yan Yosiya maza su ne, Yohanan ɗan fari, Yehohiyakim ɗa na biyu, Zedekiya ɗa na uku Shallum ɗa na huɗu.
[16] Magādan Yehohiyakim su ne, Yekoniya ɗansa, da Zedekiya.
[17] Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel,
[18] Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.
[19] ’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi. ’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce ’yar’uwarsu.
[20] Akwai kuma waɗansu biyar, Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed.
[21] Zuriyar Hananiya su ne, Felatiya da Yeshahiya, Refahiya, Arnan, Obadiya da Shekaniya.
[22] Zuriyar Shekaniya su ne, Shemahiya da ’ya’yansa maza. Hattush, Igal, Bariya, Neyariya da Shafat, su shida ne duka.
[23] ’Ya’yan Neyariya maza su ne, Eliyohenai, Hezekiya da Azrikam, su uku ne duka.
[24] ’Ya’yan Eliyohenai su ne, Hodawiya, Eliyashib, Felahiya, Akkub, Yohanan, Delahiya da Anani, su bakwai ne duka.