Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:47

[1] Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.

[2] Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.

[3] Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.

[4] Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.

[5] Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,

[6] Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.

[7] A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.

[8] Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

[9] Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.

[10] Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.

[11] Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.

[12] Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,

[13] Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.

[14] Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya.

[15] Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,

[16] alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.

[17] Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.

[18] “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.”

[19] Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,

[20] suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan.

[21] Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna.

[22] “Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.”

[23] Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.

[24] Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.

[25] Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

[26] Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai.

[27] Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.

[28] Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,

[29] ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.

[30] Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.

[31] Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”

[32] Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!

[33] Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya.

[34] Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.

[35] Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”

[36] Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”

[37] Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.

[38] Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.

[39] Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon

[40] don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.

[41] Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

[42] Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.

[43] Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.

1 Tarihi — Chapters