[1] Ubangiji ya ce wa Musa,
[2] “Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki.
[3] “ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,
[4] tă ƙetare Mashigin Kunama a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon,
[5] inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum.
[6] “ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.
[7] “ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,
[8] za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad,
[9] tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa.
[10] “ ‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam.
[11] Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.
[12] Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”
[13] Sai Musa ya umarci Isra’ilawa ya ce, “Ku raba wannan ƙasa da za ku gāda ta hanyar jefa ƙuri’a. Ubangiji ya umarta cewa a ba da ita ga kabilu tara da rabi,
[14] saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu.
[15] Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko wajen fitowar rana.”
[16] Ubangiji ya ce wa Musa,
[17] “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.
[18] Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.
[19] “Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;
[20] Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon
[21] Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;
[22] Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;
[23] Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;
[24] Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;
[25] Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;
[26] Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;
[27] Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;
[28] Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”
[29] Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.