[1] Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
[2] “Duk sa’ad da Isra’ilawa suka yi sansani, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Sansanin zai kasance a kewaye da Tentin Sujada.”
[3] Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab.
[4] Yawan mutanen sashensa 74,600 ne.
[5] Kabilar Issakar za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Netanel ɗan Zuwar.
[6] Yawan mutanen sashensa 54,400 ne.
[7] Kabilar Zebulun za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Eliyab ɗan Helon.
[8] Yawan mutanen sashensa 57,400 ne.
[9] Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Yahuda bisa ga sashensu sun kai 186,400. Su ne za su ja gaba.
[10] A kudu, a nan ne sashe sansanin mutanen Ruben a ƙarƙashin ƙa’idarsu, za su yi sansani. Shugaban mutanen Ruben shi ne Elizur ɗan Shedeyur.
[11] Yawan mutanen sashensa 46,500 ne.
[12] Kabilar Simeyon za su yi sansani biye da su. Shugaban mutanensa shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai.
[13] Yawan mutanen sashensa 59,300 ne.
[14] Kabilar Gad za su zama na biye. Shugaban mutanensa shi ne Eliyasaf ɗan Reyuwel.
[15] Yawan mutanen sashensa 45,650 ne.
[16] Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Ruben, bisa ga sashensu sun kai 151,450. Su ne za su zama na biyu in za a tashi.
[17] Sa’an nan Lawiyawa ɗauke da Tentin Sujada za su kasance a tsakiyar sansani sa’ad da aka tashi tafiya. Za su kama hanya kamar yadda aka dokace su su zauna a sansani, kowa a wurinsa a ƙarƙashin ƙa’idarsu.
[18] Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud.
[19] Yawan mutanen sashensa 40,500 ne.
[20] Kabilar Manasse ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur.
[21] Yawan mutanen sashensa 32,200 ne.
[22] Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni.
[23] Yawan mutanen sashensa 35,400 ne.
[24] Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi.
[25] A arewa za a sami sashen sansanin Dan, a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugabansu shi ne Ahiyezer ɗan Ammishaddai.
[26] Yawan mutanen sashensa 62,700 ne.
[27] Kabilar Asher ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Fagiyel ɗan Okran.
[28] Yawan mutanen sashensa 41,500 ne.
[29] Kabilar Naftali za su zama na biye da su. Shugaban mutanen kuwa shi ne Ahira ɗan Enan.
[30] Yawan mutanen sashensa 53,400 ne
[31] Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 157,600. Su ne za su zama na ƙarshe, ƙarƙashin ƙa’idarsu.
[32] Waɗannan su ne Isra’ilawan da aka a ƙidaya bisa ga iyalansu. Dukansu da suke a sansani, mutane 603,550 ne.
[33] Ba a dai ƙidaya Lawiyawa tare da sauran Isra’ilawa ba yadda Ubangiji ya umarci Musa.
[34] Saboda haka Isra’ilawa suka yi duk ko mene ne da Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka ne suka yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu kowanne tare da kabilarsa da danginsa.