Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:48

[1] Ubangiji ya ce wa Musa,

[2] “Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.”

[3] Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.

[4] Shugabannin kuwa su ne, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ruben;

[5] Shafat ɗan Hori, daga kabilar Simeyon;

[6] Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;

[7] Igal ɗan Yusuf, daga kabilar Issakar;

[8] Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;

[9] daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu;

[10] Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zebulun;

[11] Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf);

[12] Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan;

[13] Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher;

[14] Nabi ɗan Bofsi, daga kabilar Naftali;

[15] Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad.

[16] Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)

[17] Sa’ad da Musa ya aike su domin su binciki Kan’ana ya ce, “Ku haura, ku ratsa ta Negeb har zuwa ƙasar tudu.

[18] Ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanen da suke zama a can ƙarfafa ne, ko raunannu, ko su kima ne, ko kuma suna da yawa.

[19] Wace irin ƙasa ce suke zama a ciki, Mai kyau ce, ko mummuna? Waɗanne irin birane ne suke zama a ciki? Suna da katanga, ko babu?

[20] Yaya ƙasar take? Tana da wadata, ko babu? Akwai itatuwa, ko babu? Ku yi iya ƙoƙarinku ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Lokacin farkon nunan inabi ne.)

[21] Saboda haka suka haura, suka binciki ƙasar daga Hamadan Zin har zuwa Rehob, wajen Lebo Hamat.

[22] Suka kuma haura ta Negeb, suka iso Hebron, inda Ahiman, da Sheshai, da Talmai, zuriyar Anak, suke zama. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)

[23] Da suka iso Kwarin Eshkol, sai suka yanko reshe guda na nonon inabi tare da ’ya’yansa cunkus. Mutum biyu suka ɗauka shi rataye a sanda a kafaɗarsu, suka haɗa tare da rumman da kuma ɓaure.

[24] Sai aka kira wurin Kwarin Eshkol saboda nonon inabin da suka yi cunkus, wanda Isra’ilawa suka yanko a wurin.

[25] A ƙarshen kwana arba’in sai suka komo daga bincikensu.

[26] Suka dawo wurin Musa, da Haruna, da dukan jama’ar Isra’ilawa, a Kadesh, a Hamadan Faran. A can suka ba da rahoton ga dukan taron da yake wurin, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar.

[27] Suka ce wa Musa, “Mun je ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana zub da madara da zuma! Ga kuma amfaninta.

[28] Amma fa mazaunan can ɗin ƙarfafa ne, an kuma kewaye biranen da manya-manyan katanga. Mun kuma ga zuriyar Anak a can.

[29] Amalekawa suna zama a Negeb; Hittiyawa, Yebusiyawa da kuma Amoriyawa, suna zama ne a ƙasar tudu. Kan’aniyawa kuma suna zama kusa da teku da kuma a bakin Urdun.”

[30] Sai Kaleb ya sa mutane suka yi shiru a gaban Musa, sai ya ce, “Ya kamata mu tafi mu mallaki ƙasar, gama lalle za mu iya cinta.”

[31] Amma sauran mutanen da suka je tare da shi, suka ce, “Ba za mu iya kara da mutanen nan ba; sun fi mu ƙarfi.”

[32] Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne.

[33] Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”

Ƙidaya — Chapters