[1] Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa,
[2] waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada.
[3] Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.
[4] Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”
[5] Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”
[6] Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada.
[7] Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi
[8] ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa.
[9] Waɗanda suka mutu a wannan annoba, sun kai mutum 24,000.
[10] Ubangiji ya ce wa Musa,
[11] “Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba.
[12] Saboda haka ka faɗa masa cewa zan yi alkawarin salama da shi.
[13] Shi da zuriyarsa za su kasance da alkawari na zama firist har abada, saboda kishinsa domin ɗaukakar Allahnsa, ya kuma yi kafara domin Isra’ilawa.”
[14] Sunan mutumin Isra’ilan da aka kashe tare da macen nan Bamidiyana kuwa Zimri ne, ɗan Salu, shugaban mutanen Simeyon.
[15] Sunan macen nan Bamidiyana da aka kashe kuwa Kozbi ne, ’yar Zur, wani basaraken iyalin Midiyawa.
[16] Ubangiji ya ce wa Musa,
[17] “Ka ɗauki Midiyawa a matsayin abokan gāba, ka kuma kashe su,
[18] gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da ’yar’uwarsu Kozbi ’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.”