Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 8:08

[1] Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.

[2] Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance.

[3] Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa,

[4] waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.

[5] Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.

[6] Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.

[7] Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.

[8] Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.

[9] Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.

[10] Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.

[11] Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.

[12] Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.

[13] Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.

[14] Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.

[15] Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.

[16] Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa.

[17] Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot.

[18] Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma.

[19] Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez.

[20] Suka tashi daga Rimmon Ferez, suka yi sansani a Libna.

[21] Suka tashi daga Libna, suka yi sansani a Rissa.

[22] Suka tashi daga Rissa, suka yi sansani a Kehelata.

[23] Suka tashi daga Kehelata, suka yi sansani a Dutsen Shefer.

[24] Suka tashi daga Dutsen Shefer, suka yi sansani a Harada.

[25] Suka tashi daga Harada, suka yi sansani a Makhelot.

[26] Suka tashi daga Makhelot, suka yi sansani a Tahat.

[27] Suka tashi daga Tahat, suka yi sansani a Tera.

[28] Suka tashi daga Tera, suka yi sansani a Mitka.

[29] Suka tashi daga Mitka, suka yi sansani a Hashmona.

[30] Suka tashi daga Hashmona, suka yi sansani a Moserot.

[31] Suka tashi daga Moserot, suka yi sansani a Bene Ya’akan.

[32] Suka tashi daga Bene Ya’akan, suka yi sansani a Hor Haggidgad.

[33] Suka tashi daga Hor Haggidgad, suka yi sansani a Yotbata.

[34] Suka tashi daga Yotbata, suka yi sansani a Abrona.

[35] Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber.

[36] Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin.

[37] Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.

[38] Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar.

[39] Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.

[40] Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa.

[41] Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona.

[42] Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon.

[43] Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot.

[44] Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab.

[45] Suka tashi daga Iyim, suka yi sansani a Dibon Gad.

[46] Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim.

[47] Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.

[48] Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.

[49] A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim.

[50] A filayen Mowab kusa da Urdun ɗaura da Yeriko ne Ubangiji ya ce wa Musa,

[51] “Ka gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana,

[52] ku kori dukan mazaunan ƙasar a gabanku. Ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsu, da siffofinsu na zubi, ku kuma rurrushe dukan masujadansu na kan tudu.

[53] Ku mallaki ƙasar, ku kuma zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.

[54] Ku rarraba ƙasar ta wurin jefan ƙuri’a, bisa ga kabilanku. Kabilar da take babba, a ba ta babban gādo, ƙarami kabila kuwa, a ba ta ƙaramin gādo. Duk abin da ƙuri’a ta ba su, shi zai zama nasu. Ku rarraba wannan bisa zuriyar kakanninku.

[55] “ ‘Amma in ba ku kori mazaunan ƙasar ba, waɗanda kuka bari su ci gaba da zama, za su zama muku hakki a idanunku, da kuma ƙayayyuwa a bayanku. Za su ba ku wahala a ƙasar da kuke zama.

[56] Sa’an nan kuwa zan yi muku abin da na shirya yin musu.’ ”

Ƙidaya — Chapters