Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:33

[1] Ubangiji ya ce wa Musa,

[2] “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa.

[3] A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.

[4] Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai.

[5] Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.”

[6] Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.

[7] Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.

[8] Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ’ya’yan almon.

[9] Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.

[10] Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”

[11] Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.

[12] Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan!

[13] Idan an ce duk wanda ya zo kusa da tabanakul na Ubangiji zai mutu, ai rayuwarmu kamar mun mutu ke nan.”

Ƙidaya — Chapters