Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:53

[1] Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura.

[2] Suka ce, “Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai? Ashe, bai yi magana ta wurinmu mu ma ba?” Ubangiji kuwa ya ji wannan.

[3] (Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.)

[4] Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi.

[5] Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,

[6] sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai.

[7] Amma ba haka nake magana da Musa bawana ba; na sa shi yă lura da dukan jama’ata Isra’ila.

[8] Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?”

[9] Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su.

[10] Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;

[11] sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta.

[12] Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.”

[13] Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!”

[14] Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.”

[15] Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita.

[16] Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran.

Ƙidaya — Chapters