[1] Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata,
[2] sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.
[3] Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”
[4] Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.
[5] Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.
[6] Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.
[7] Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
[8] Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
[9] Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.
[10] Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
[11] Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.
[12] Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.
[13] Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.
[14] Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires, ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje.
[15] Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45.
[16] Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.
[17] Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka.
[18] Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai.
[19] Za ka shigar da biyu na dukan halittu masu rai, namiji da ta mace a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai.
[20] Biyu na kowane irin tsuntsu, kowace irin dabba da kuma kowace irin halitta mai rarrafe a ƙasa, za su zo wurinka domin a bar su da rai.
[21] Za ka ɗauki kowane irin abinci wanda za a ci, ka adana don yă zama abincinka da nasu.”
[22] Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.