[1] Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.
[2] Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa.
[3] Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
[4] Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai,
[5] babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar,
[6] amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa.
[7] Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
[8] To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi.
[9] Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.
[10] Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu.
[11] Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.
[12] (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.)
[13] Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush.
[14] Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.
[15] Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
[16] Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun,
[17] amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”
[18] Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
[19] To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan.
[20] Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye. Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba.
[21] Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama.
[22] Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
[23] Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”
[24] Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
[25] Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.