[1] Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya.
[2] Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.
[3] Sai Ibrahim ya tashi daga gefen matarsa da ta mutu, ya yi magana da Hittiyawa. Ya ce,
[4] “Ni baƙo ne, kuma baƙo a cikinku. Ku sayar mini da wani wuri yă zama wurin binnewa a nan, domin in binne mataccena.”
[5] Hittiyawa suka ce wa Ibrahim,
[6] “Ranka yă daɗe, ka saurare mu. Kai babban yerima ne a cikinmu. Ka binne mataccenka a kabari mafi kyau na kaburburanmu. Babu waninmu da zai hana ka kabarinsa don binne mataccenka.”
[7] Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna a gaban mutanen ƙasar, wato, Hittiyawan.
[8] Ya ce musu, “In kuna so in binne mataccena, sai ku ji ni, ku roƙi Efron ɗan Zohar a madadina
[9] domin yă sayar mini da kogon Makfela, wanda yake nasa, wannan da yake a ƙarshen filinsa. Ku ce masa yă sayar mini a cikakken farashi, yă zama mallakata domin makabarta tsakaninku.”
[10] Efron mutumin Hitti yana zaune a cikin mutanensa, sai ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birni.
[11] Ya ce, “A’a, ranka yă daɗe, ka ji ni, na ba ka filin, na kuma ba ka kogon da yake cikinsa. Na ba ka shi a gaban mutanena. Ka binne mataccenka.”
[12] Ibrahim ya sāke rusuna a gaban mutanen ƙasar
[13] ya ce wa Efron a kunnuwansu, “Ka ji, in ka yarda. Zan biya farashin filin. Ka karɓa daga gare ni don in iya binne mataccena a can.”
[14] Efron ya ce wa Ibrahim,
[15] “Ka saurare ni, ranka yă daɗe; darajan filin ya kai shekel ɗari huɗu na azurfa, amma mene ne wannan a tsakanina da kai? Ka binne mataccenka.”
[16] Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin.
[17] Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka
[18] ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin.
[19] Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana.
[20] Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta.