[1] Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa.
[2] Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!” Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
[3] Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can.
[4] Zan gangara zuwa Masar tare da kai, tabbatacce zan sāke dawo da kai. Kuma hannun Yusuf zai rufe idanunka.”
[5] Sa’an nan Yaƙub ya bar Beyersheba, ’ya’yan Isra’ila maza, suka ɗauki mahaifinsu Yaƙub da ’ya’yansu da matansu a cikin wagonun da Fir’auna ya aika don a kawo shi.
[6] Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar.
[7] Ya ɗauki ’ya’yansa maza da jikokinsa da ’ya’yansa mata da jikokinsa mata, dukan zuriyarsa zuwa Masar.
[8] Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar, Ruben ɗan farin Yaƙub.
[9] ’Ya’yan Ruben maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
[10] ’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana.
[11] ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
[12] ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
[13] ’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yoshub da Shimron.
[14] ’Ya’yan Zebulun maza su ne, Sered, Elon da Yaleyel.
[15] Waɗannan su ne ’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da ’yarsa Dina. ’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne.
[16] ’Ya’yan Gad maza su ne, Zafon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli.
[17] ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishbi da Beriya. ’Yar’uwarsu ita ce Sera. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel.
[18] Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne.
[19] ’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin.
[20] A Masar, Asenat ’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf.
[21] ’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard.
[22] Waɗannan su ne ’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne.
[23] Yaron Dan shi ne, Hushim.
[24] ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yazeyel, Guni, Yezer da Shillem.
[25] Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne.
[26] Dukan waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub, waɗanda suke zuriyarsa kai tsaye ban da matan ’ya’yansa maza, su mutum sittin da shida ne.
[27] In aka haɗa da ’ya’yan nan maza guda biyu waɗanda aka haifa wa Yusuf a Masar, membobin iyalin Yaƙub, waɗanda suka tafi Masar, duka su saba’in ne.
[28] To, Yaƙub ya aiki Yahuda yă yi gaba yă sadu da Yusuf, don yă nuna musu hanyar da za su bi zuwa yankin Goshen. Da suka isa yankin Goshen,
[29] sai Yusuf ya kintsa keken yaƙinsa ya haura zuwa Goshen don yă taryi mahaifinsa, Isra’ila. Nan da nan da isowar Yusuf a wurin mahaifinsa, sai ya rungumi mahaifinsa, ya yi kuka na dogon lokaci.
[30] Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Yanzu ina a shirye in mutu, da yake na gani da kaina cewa har yanzu kana da rai.”
[31] Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa da gidan mahaifinsa, “Zan haura in yi magana da Fir’auna, zan kuwa ce masa, ‘’Yan’uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke zaune a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina.
[32] Mutanen fa, makiyaya ne; suna kiwon dabbobi, sun kuma zo tare da garkunansu da shanunsa da kuma kome da suka mallaka.’
[33] Sa’ad da Fir’auna ya kira ku ciki, ya yi tambaya, ‘Mece ce sana’arku?’
[34] Ku amsa, ‘Bayinka suna kiwon dabbobi ne, tun muna samari har zuwa yanzu, kamar yadda kakanninmu suka yi.’ Ta haka za a bar ku ku zauna a yankin Goshen, gama Masarawa suna ƙyamar makiyaya.”