Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 9:00

[1] Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).

[2] Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye

[3] ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot.

[4] Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.

[5] Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.

[6] Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.

[7] Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu.

[8] Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.

[9] Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.

[10] Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza, Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.

[11] ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.

[12] Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.

[13] ’Ya’yan Reyuwel maza su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.

[14] ’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne, Yewush, Yalam da Kora.

[15] Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,

[16] Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.

[17] ’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.

[18] ’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa.

[19] Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.

[20] Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,

[21] Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.

[22] ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce.

[23] ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.

[24] ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.

[25] ’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama ’yar Ana.

[26] ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.

[27] ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.

[28] ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.

[29] Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,

[30] Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.

[31] Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,

[32] Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.

[33] Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.

[34] Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.

[35] Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.

[36] Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.

[37] Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi.

[38] Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.

[39] Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.

[40] Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet.

[41] Oholibama, Ela, Finon.

[42] Kenaz, Teman, Mibzar.

[43] Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.

Farawa — Chapters