[1] Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
[2] ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
[3] ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
[4] ’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
[5] (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
[6] ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
[7] ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan.
[8] Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
[9] Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
[10] Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
[11] Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala
[12] da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
[13] Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa,
[14] Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
[15] Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
[16] Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
[17] Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
[18] Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu
[19] har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
[20] Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
[21] Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
[22] ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
[23] ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.
[24] Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
[25] Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
[26] Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,
[27] Hadoram, Uzal, Dikla,
[28] Obal, Abimayel, Sheba,
[29] Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
[30] Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
[31] Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
[32] Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.