[1] Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.
[2] Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”
[3] Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
[4] Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
[5] Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
[6] Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.
[7] Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
[8] Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
[9] Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.
[10] Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
[11] Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
[12] Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel.
[13] Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
[14] Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
[15] Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared.
[16] Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
[17] Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
[18] Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.
[19] Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
[20] Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
[21] Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela.
[22] Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
[23] Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365.
[24] Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
[25] Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek.
[26] Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
[27] Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
[28] Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa.
[29] Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”
[30] Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata.
[31] Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
[32] Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.