[1] Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
[2] “Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari.
[3] Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.
[4] Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa.
[5] Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.
[6] “Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada;
[7] ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa.
[8] Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
[9] “Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake.
[10] Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.
[11] Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
[12] “Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa.
[13] Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.
[14] Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.
[15] Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”
[16] Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.
[17] Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu.
[18] Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan.
[19] Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
[20] Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa.
[21] Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
[22] Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.
[23] Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
[24] Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul
[25] ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
[26] Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen
[27] ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.
[28] Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul.
[29] Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
[30] Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki,
[31] a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.
[32] Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
[33] Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.
[34] Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul.
[35] Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.
[36] Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.
[37] Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.
[38] Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.