Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:33

[1] To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya.

[2] Ka faɗa wa mutane cewa dukan maza da mata, su roƙi maƙwabtansu kayan azurfa da na zinariya.”

[3] (Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.)

[4] Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar.

[5] Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu.

[6] Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba.

[7] Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila.

[8] Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.

[9] Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna zai ƙi kasa kunne gare ka, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin Masar.”

[10] Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu’ujizai a gaban Fir’auna, amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa ba.

Fitowa — Chapters