Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:21

[1] Bezalel ya yi akwatin alkawari da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

[2] Ya dalaye shi da zinariya zalla, ciki da waje, ya kuma yi zubin zinariya kewaye da shi.

[3] Ya yi masa zubi huɗu na zoban zinariya, ya kuma ɗaura su a ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a wannan gefe da kuma biyu a wancan.

[4] Sa’an nan ya yi sanduna na itacen ƙirya, ya dalaye shi da zinariya.

[5] Sai ya sa sandunan a cikin rammukan da suke gefen Akwatin don ɗaukarsa.

[6] Ya yi murfin jinƙai da zinariya zalla, wato, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi.

[7] Sa’an nan ya yi kerubobi biyu da ƙeraren zinariya a ƙarshen murfin jinƙan.

[8] Ya yi kerub a iyakar gefe ɗaya, ya yi ɗayan kuma a wancan gefe; a iyakan nan biyu, ya yi su a haɗe da murfin.

[9] Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwatar da murfin da fikafikansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kuma kallon murfin.

[10] Suka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa ƙafa ɗaya, tsayinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi.

[11] Sa’an nan suka dalaye shi da zinariya zalla, suka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.

[12] Suka kuma yi masa baki mai fāɗin tafi hannu, suka yi zubin zinariya a bisa bakin.

[13] Suka yi zubin zobai huɗu na zinariya don tebur ɗin, sai suka ɗaura su a kusurwoyi huɗu inda ƙafafu huɗun suke.

[14] Sa’an nan aka sa zoban kurkusa da bakin don riƙe sandunan da ake amfani da su wurin ɗaukan teburin.

[15] An yi sandunan da ake ɗaukan tebur da itacen ƙirya, aka kuma dalaye su da zinariya.

[16] Suka kuma yi duk kayayyakin teburin da zinariya zalla, farantansa, kwanonin tuya, kwanoninsa, da kuma butoci domin hadaya ta sha.

[17] Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan.

[18] Akwai rassa guda shida da suka miƙe daga gefe wurin ajiyar fitilar, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.

[19] A reshe guda na wurin ajiye fitilan, akwai kwaf uku masu kama da tohon almon, akwai kuma uku a reshe na biye, haka kuma suke a dukan rassa shida da suke daga wurin ajiye fitilan.

[20] A bisa wurin ajiye fitilan kuma akwai kwaf huɗu da aka yi su kamar furannin almon da toho da kuma mahaɗai.

[21] Toho ɗaya yana a ƙarƙashin rassa biyu waɗanda suke daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu yana a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku kuma yana a ƙarƙashin rassa biyu na uku, duka-duka rassa shida ne.

[22] An ƙera mahaɗai da rassa wurin ajiye fitila a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi wurin ajiye fitilar da dukan komensa a haɗe.

[23] Da zinariya zalla suka yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa.

[24] Daga talenti ɗaya na zinariya zalla suka yi wurin ajiye fitila da dukan kayayyakinsa.

[25] Suka yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya. Shi bagaden, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu biyu, ƙahoninsa kuwa a haɗe suke da shi.

[26] Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi.

[27] Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi.

[28] Suka yi sandunan da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da zinariya.

[29] Suka kuma yi tsattsarkan mai na shafewa da kuma zalla turare mai ƙanshi, yadda mai yin turare yakan yi.

Fitowa — Chapters