Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 7:47

[1] Ubangiji ya ce wa Musa,

[2] “Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar.

[3] “Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu, “zinariya, da azurfa, tagulla,

[4] shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya,

[5] fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau, itacen akashiya,

[6] mai domin fitila, kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,

[7] da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

[8] “Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu.

[9] Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.

[10] “Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

[11] Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya.

[12] Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe.

[13] Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.

[14] Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa.

[15] Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba.

[16] Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.

[17] “Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

[18] Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin.

[19] Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya.

[20] Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.

[21] Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki.

[22] Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.

[23] “Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

[24] Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.

[25] Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

[26] Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke.

[27] Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin.

[28] Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin.

[29] Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu.

[30] Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum.

[31] “Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi.

[32] Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen.

[33] Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan.

[34] A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni.

[35] Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka.

[36] Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.

[37] “Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.

[38] Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya.

[39] Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka.

[40] Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.

Fitowa — Chapters